Mr. Kim wanda babban wakili ne a ofishin kwance damara na MDD, ya kara da cewa yayin taro na 4 na tsaron nukiliya da ya gudana a birnin Washington, kasar Sin ta bada cikakkiyar gudummawa da ta dace.
Kaza lika a cewar sa, Sin na kara daukar matakan inganta tsaron nukiliya, ciki hada kafa cibiyar tsaron nukilaya, da karfafa dokokin cikin gidan ta a fannin, tare da kididdige sinadaran nukiliya, da sauran matakan da ke da fa'ida.