in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da cibiyar tsaron nukiliya na Sin da Amurka
2016-03-18 21:25:44 cri
An kaddamar da cibiyar tsaron nukiliya mafi girma a yankin Asia da fasifik, da kasashen Sin da Amurka suka dauki nauyin ginawa a ranar Jumma'ar nan, kamar yadda mahukuntan kasashen biyu suka tabbatar.

Cibiyar, wanda hukumar makamashin atomic na kasar Sin da sashin makamashi na Amurka suka gina, zai iya horas da kusan jami'an tsaro a harkar nukuliya guda dubu biyu ma kasar Sin da sauran kasashen yankin Asia da Fasifik a ko wace shekara, in ji Shugaban hukumar makamashin atomic na kasar Sin Xu Dazhe.

Gina cibiyar, wanda shi ne shirin nukiliya mafi girma da ya samu tallafin kudi kai tsaye daga Amurka da Sin an fara shi tun daga shekara ta 2013.

A cewar hukumar, cibiyar nukiliyar na da alhakin yin musayar jami'ai na kasa da kasa da kuma yin hadin gwiwwa a kan tsaron nukiliya, koyar da dabarun fasashohin zamani da kuma gwajin da tantancewa ba da horon ilimi.

Cibiyar ya kafa wani muhimmin cigaba a hadin gwiwwar tsaron nukiliya tsakanin Sin da Amurka kuma zai habaka hadin gwiwwa a yankin Asia da Fasifik da ma duniya baki daya, inji Wang Yiren, mataimakin hukumar ta kasar Sin

Haka kuma zai inganta amfani da karfin nukiliya cikin lumana, inji Mr Wang wanda kuma shi ne mataimakin sashin mulki na kimiyya, fasaha da masana'antu na tsaron kasa.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China