in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a daidaita batutuwan da suka shafi hana yaduwar makaman nukiliya yadda ya kamata
2016-08-24 11:22:33 cri
A jiya Talata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mr. Liu Jieyi ya yi kira da a daidaita batun nukiliyar zirin Koriya da dai sauran batutuwan da suka shafi hana yaduwar makaman nukiliya yadda ya kamata, kuma kada a dauki matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki.

A wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da babbar muhawara dangane da hana yaduwar makaman nukiliya. A yayin da yake gabatar da jawabi, Mr. Liu Jieyi ya ce, kamata ya yi bangarori daban daban su nace ga tabbatar da rashin kasancewar makaman nukiliya tare da kiyaye zaman lafiya a zirin Koriya, sa'an nan a nace ga daidaita batun ta hanyar yin shawarwari, a kuma kaucewa daukar matakai domin kalubalantar juna, lamarin da ka iya tsananta halin da ake ciki, ciki har da batun kara jibge sojoji da habaka ayyukan atisayen soja bisa ga dalili na hana yaduwar makaman nukiliya.

Liu Jieyi ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan hana yaduwar manyan makaman kare dangi da kuma na'urorin jigilarsu, kuma tana kokarin sauke nauyin da ke wuyanta na hana yaduwar makaman nukiliya a duniya tare da yin hadin gwiwa da kasa da kasa. Kasar Sin tana goyon bayan kokarin da ake yi na kafa yankin rashin kasancewar makaman nukiliya, kuma ta riga ta amince da yarjejeniyar yankin rashin kasancewar makaman nukiliya a tsakiyar Asiya, ta kuma daidaita daukacin matsalolin da yarjejeniyar yankin rashin kasancewar makaman nukiliya a kudu maso gabashin Asiya da suka rage tare da kasashen ASEAN, kuma tana fatan za a daddale yarjejeniyar da wuri. Kasar Sin tana kuma goyon bayan gudanar da taron kasa da kasa a kan rashin kasancewar makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China