Mr. Fayemi wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce hakan na da nasaba da kwazon da kamfanin siminti na Dangote ya nuna a fannin zuba jari, karkashin tsare tsaren da gwamnatin tarayyar kasar ke marawa baya. Ya ce abun alfahari ne ganin cewa a baya Najeriyar na shigo da kaso kusan 60 bisa 100 na simintin da ake bukata a cikin kasar daga ketare, amma yanzu ta kai ana fitar da shi zuwa kasashen waje.
Ministan wanda ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa kamfanin Simintin na Dangote dake Ibese a jihar Ogun dake kudancin Najeriya, ya ce gwamnatin kasar mai ci, na farin ciki da rawar da kamfanin ke takawa wajen bunkasa sana'ar samar da Siminti a kasar.
A watan Fabarairun da ya shude ne, babban manajan daraktan kamfanin Onne Van der Weijde, ya bayyana cewa, bisa alkaluman kididdigar hajoji da ribar da kamfanin ya samu a shekarar 2016, kamfanin na fitar da kusan tan dubu dari hudu na Simintinsa zuwa kasashe makwaftan Najeriya. (Saminu Hassan)