Babban jami'in gudanarwar kamfanin man fetur na kasar NNPC Saidu Mohammed, ya bayyana hakan ne a Abuja, bayan kammala wani sabon tsarin kasuwanci na musamman a kamfanin samar da iskar gas na kasar, ya ce tashoshin lantarkin, za'a gina su ne da hadin gwiwar kamfanonin samar da lantarki na kasa da kasa, da masu zuba jari na Najeriyar.
Kamfanin zai samar da hasken lantarki mai karfin megawatts 4,000 nan da shekaru 10 masu zuwa, domin wadata kasar da hasken lantarki, ya kara da cewa, samar da hasken lantarki kasuwanci ne mai girman gaske.
Ya ce kamfanin ya tsara wasu hanyoyin sarrafawa, yin sufuri da kuma cinikin iskar gas a cikin kasar dama fitarwa kasashen waje, ya kara da cewa fannin iskar gas na kasar zai iya kawo sauyi wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.(Ahmad Fagam)