in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kaddamar da sabbin ka'idojin shigi da fici
2017-03-21 09:48:17 cri
A jiya Litinin, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabbin dokokin shigi da fici da nufin inganta sha'anin tsaro da kuma saukakawa masu sha'awar kasuwanci a kasar, sabbin dokokin sun tanadi wasu sauye sauye da suka shafi harkokin shigi da fici a kasar wadan da za'a aiwatar da su a zahiri.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriyar Abdulrahman Dambazau, ya ce sabon daftarin wanda aka yiwa taken "dokokin shigi da fici na 2017" an kaddamar da shi ne a Abuja, kuma zai maye tsohon tsarin dokokin shigi da fici na kasar wanda ake amfani da shi tun a shekarar 1963.

Dambazau ya ce, sabbin dokokin zasu taimakawa kasar wajen binciken kwa-kwaf a kan iyakokin shiga kasar domin zakulo bata gari, da masu alaka da ayyukan ta'addanci.

Ministan ya shedawa jami'an diplomasiyya da kusoshin gwamnati cewa, tsoffin dokokin shigi da ficin na 1963, ba su tanadi batutuwa irin na zamani ba, musamman batutuwan da suka shafi ta'addanci, sabbin fasahohin zamani da kuma manyan sabbin kalubaloli da suka shafi harkokin shigi da da fici.

Ya kara da cewa sabbin dokokin, za su baiwa hukumar kula da shigi da fici ta Najeriyar damar yin registar dukkan baki 'yan kasashen waje, da kare kan iyakokin kasar, da inganta sha'anin tsaron cikin gida, kuma zai janyo hankulan masu zuba jari daga kasashen waje ta hanyar amfani da fasahar zamani.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China