Ana dai gudanar da aikin noma da damuna a sassan Najeriya, kuma a 'yan yankunan gonaki kadan ne ake iya jan ruwa domin noma da rani. Saboda haka, masana a fannin ke bayyana cewa, bai kamata a ci gaba da dogoro kan ruwan sama ba, kuma rashin karfafa noman rani, dai haifar da rashin tabbas ga samar da isasshen hatsi, balle har a cimma burin kara yawan hatsin da kasar ke samarwa.
An dai yi hasashen cewa, Najeriya na fuskantar kalubale wajen samar da hatsi a bana sakamakon yanayi na karancin ruwan sama. (Bilkisu)