in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
2017-03-21 20:41:34 cri
A yau Talata a nan birnin Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gana da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda suka shelanta cewa, za a kafa dangantakar abokantaka irinta kirkire-kirkire masu zurfi daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu.

Da yake tsakoci, Xi Jinping ya nuna cewa, dangantakar abokantaka irinta kirkire-kirkire masu zurfi daga dukkan fannoni, za ta kara ingiza kasashen Sin da Isra'ila, su sabunta hadin gwiwar yin kirkire-kirkire a tsakanin su, ta yadda za su iya kara taimakawa juna, wajen kawo wa al'ummominsu karin moriya irin ta a zo a gani.

A nasa bangare Mr. Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, kasar Isra'ila za ta ci gaba da bin manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, kuma tana fatan yin amfani da wannan dama, ta kafa huldar abokantaka irinta kirkire-kirkire a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu, ta yadda kasashen biyu za su iya yin amfani da karfinsu na kirkiro sabbin fasahohin zamani, domin kara hadin gwiwa a fannonin samar da makamashi maras gurbata muhalli, da aikin gona, da zuba jari, da hada hadar kudi da ba da jinya, ta yadda za a iya kawo wa al'ummomin kasashen biyu alheri, tare da ma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa duniya gaba daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China