A jawabinsa yayin bikin da ya gudana a dakin adana kayan yaki na tarihi na kasar Sin, mamban dindindin a hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis na kasar Sin Liu Yunshan ya ce, bikin wata dama ce ta nuna abubuwan tarihi, da tunawa da dakarun da suka kwanta dama da kuma murnar samun zaman lafiya.
Bugu da kari bikin wani bangare ne na kammala bikin cika shekaru 70 da samun nasarar a kan sojojin Japan da kuma nasarar yakin duniya na biyu, wanda kuma ake fatan kammala shi da wani kasaitaccen fareti a ranar 3 ga watan Satumba a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Har ila Mr. Liu ya ce, bikin wata kafa ce ta ilimantar da jama'a game da bukatar nuna kishin kasa da kare kai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Don haka, ya bukaci daukacin Sinawa da su tashi tsaye don ganin kasar ta cimma mafarkinta na bunkasa zaman lafiya da ci gaba. (Ibrahim)