Shugaban hukumar kula da harkokin yin cudanya da jami'yyun siyasa na kasashen ketare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Song Tao, ya halarci bikin bude taron, inda ya bayyana cewa, ya kamata jam'iyyun kasar Sin da kasashen Afirka su nuna kwazo wajen neman hanyoyin bunkasuwa, da kuma inganta harkokin yin shawarwari kan fasahohin neman cigaba a tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a ciyar da hadin gwiwar Sin da Afirka gaba.
Kaza lika, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son habaka sabbin hanyoyin yin shawarwari da mu'amala bisa fannonin daban daban a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, haka kuma, ana son zurfafa shawarwarin dake tsakanin jam'iyyun kasar Sin da kasashen Afirka ta hanyar yin taron karawa juna sani kan harkokin jam'iyyun siyasa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Maryam)