in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi watsi da baiwa Ilham Tohti lambar yabo ta kare hakkin bil'adama
2016-10-12 19:55:38 cri
Kasar Sin ta yi matukar nuna rashin gamsuwa da baiwa dan-awaren nan Basine mai suna Ilham Tohti lambar karramawa, wadda cibiyar Martin Ennals ke bayarwa ga wadanda suka yi fice a fannin kare hakkin bil'adama.

An dai tabbatarwa Tohti lambar ne a wani biki da babban kwamishinan MDD mai kula da harkar kare hakkin bil'adama Ra'ad Al-Hussein ya halarta, a ranar Talata a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce an yankewa Tohti wanda malami ne dan kabilar Urgur hukuncin daurin rai da rai a shekarar 2014, bayan da aka tabbatar da zargin da aka yi masa na aikata laifuka masu alaka da ta'addanci, da raba kawunan al'umma da rura wutar rikici, laifukan da babu wata kasa da za ta amince da su.

Mr. Geng ya ce an yankewa Tohti hukunci ne bisa dalilai na shari'a, da suka dace da dokokin kasar Sin, kuma bai dace wani yayi kutse cikin lamarin shari'a, ko harkokin cikin gidan kasar Sin ba.

Geng ya ce halartar kwamishinan MDD wannan biki, ya sabawa ka'idojin MDDr, da ma tanaje-tanajen ta, ya kuma kasance tamkar tsoma hannu ne cikin harkokin kasar Sin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China