Ministan noma da raya karkara na kasar Audu Ogbeh shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Legas, ya ce Najeriyar za ta fara fitar da 'ya'yan kanju da aka sarrafa zuwa kasashen ketare nan da shekarar 2019, ya ce a halin yanzu ton guda na 'ya'yan kanju da aka sarrafa ya kai dala dubu 10 a kasuwannin duniya.
Ya kara da cewa ya fi dacewa a fitar da 'ya'yan kanju da aka sarrafa zuwa kasashen ketare a maimakon wanda ba'a sarrafa shi ba.
Ogbeh ya ce gwamnatin kasar tana bin matakan da suka dace domin ganin 'ya'yan kanju sun samu karbuwa a kasuwannin duniya. (Ahmad Fagam)