in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwa mutane 7 a Nijeriya
2017-03-20 10:18:14 cri
Jiya Lahadi, rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa, an kai wani harin kunar bakin wake a daren ranar 18 ga wata a karkarar Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Harin ya haddasa rasuwar mutane 7, ciki har 'dan kunar bakin waken, tare da raunana wasu guda 8.

Yanzu haka dai wadanda suka jikkata na jinya a asibitin dake kusa da wurin.

Kawo yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China