Shugaban ofishin hulda da jama'a na birnin Addis Ababa Dagmawit Moges ya bayyana cewa, adadin mutane da suka mutu yana iya karuwa yayin da ake ci gaba da aikin zakulo wadanda suke da sauran numfashi a wurin da bala'in ya faru.
A ranar Asabar da dare ne dai tabo da sauran tarkace suka gangaro daga babban wurin zubar da sharar da aka kwashe shekaru kusan hamsin ana amfani da shi, lakar da ta gangaro ta rufe gidaje baya ga wasu mazauna wurin da dama da ake fargabar sun bace.
Magarin garin birnin Addis Ababa Diriba Kuma, ya shaidawa manema labarai a jiya Lahadi da safe cewa, ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto tare da neman mutanen da suka bace tun lokacin aukuwar lamarin da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar agogon wurin. (Ibrahim)