Adadin yawan mutanen da suka rasu sakamakon hadarin rubzawar laka a wajen birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya zarce mutum 50. Da yake karin haske ga wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin game da hakan, shugaban ofishin watsa labarai na hukumar birnin Addis Ababa Dagmawit Moges, ya ce yawan wadanda suka jikkata yayin hadarin na daren ranar Asabar ya kai mutum 28, ciki hadda 2 dake cikin hali na rai kokwai mutu kokwai.
Mr. Dagmawit, ya kara da cewa, mai yiwuwa ne wannan adadi ya karu, yayin da ake ci gaba da zakulo sauran wadanda suka bace a wurin da lakar ta zaftare.
Cikin matakan da mahukuntan yankin suka dauka domin kaucewa sake aukuwar wannan hadari dai a yanzu haka, sauyawa wasu mutane da yawan su ya kai 300 matsugunai, daga yankin dake daura da inda hadarin ya auku.