in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya koma bakin aiki bayan dawowarsa kasar daga hutun jinya
2017-03-14 09:13:06 cri
A jiya Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki, bayan ya sanar da majaliar dokokin kasar a rubuce cewa, ya dawo daga dogon hutun jinyar da ya yi a kasar Burtaniya.

Wata sanarwar da kakakin fadar shugaban kasar Femi Adesina ya rabawa manema labarai ta kuma bayyana cewa, shugaban ya rubuta wasikar ce kamar yadda sashi na 145 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 da aka yiwa gyaran fuska ya tanada.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce dai shugaba Buharin ya dawo gida, inda ya samu gagarumar tarba daga 'yan Najeriya. A jawabinsa jim kadan bayan isarsa fadar ta Aso Rock dake Abuja, fadar mulkin Kasar, shugaba Buhari ya godewa 'yan kasar da irin addu'o'in fatan alheri da suka yi masa a lokacin da yake jinya. Yana mai alkawarin kara zage damtse wajen sauke nauyin da suka dora masa.

Ya ce, ya samu sauki sosai, amma kuma a 'yan wasu makonni zai fita waje domin a sake duba lafiyarsa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China