in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun ceto mutane 455 da mayakan Boko Haram ke garkuwa da su
2017-03-15 09:27:44 cri
A kalla mutane 455 ne suka kubuta daga hannun mayakan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya bayan da sojojin kasar suka yiwa mayakan 'yan ta'addan dirar mikiya a Litinin din da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Sani Usman ya ce, an ceto mutane ne a a ranar Litinin a lardin Kala Balge dake jihar Borno, bayan da dakarun Najeriya suka kai samame a maboyar 'yan ta'addan bayan munanan hare-hare da dakarun sojin suka kaddamar kan 'yan ta'addan.

Sanarwar ta kara da cewa, tuni aka tura mutanen da aka ceto zuwa sansanonin 'yan gudun hijira a jihar ta Borno.

A cewar Usman 'yan ta'addan da dama sun yi kokarin kare kansu a lokacin da dakarun sojin suka afka musu a yankin na Kala Balge. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China