Michael Moller: Ziyarar shugaba Xi ya sake bayyana goyon baya da Sin take bayarwa ga ayyukan MDD
Daga ranar 15 zuwa 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Switzerland, tare da halartar taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya(WEF) na shekarar 2017 a Davos. A yayin ziyarar, ana saran shugaba Xi zai kai ziyara ofishin MDD dake Geneva. Game da wannan batu, babban darektan ofishin MDD a Geneva, Michael Moller ya bayyana wa 'yan jarida a fadar Nations a Geneva a kwanan baya cewa, ziyarar shugaba Xi ta sake bayyana cewa, Sin tana nuna goyon baya sosai ga tsarin kasancewar bangarori da dama da MDD ke kiyaye da da ayyukan da MDD ke gudanarwa.
Michael Moller ya yabawa kasar Sin bisa ga taka rawar a zo a gani a dandalin duniya da harkoki tsakanin kasashe da dama. Ya ce, MDD tana dora muhimmanci kan gudummawa da babban tasiri da Sin ta yi a cikin harkokin duniya, da fatan bangarorin biyu za su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)