An bude gasar tuka keke ta bana ne a ranar 11 ga watan Maris, kuma hanyar da aka yi gasar ta kai tsawon kilomita 956.7, inda ta ratsa manyan yankuna biyar na kasar Kamaru.
Shugaban kungiyar masu tuka keke ta Kamaru, wadda da ta shirya gasar, Ornoch Yossi, ya yaba da yadda aka gudanar da gasar, inda ya ce, a wannan karo, an gayyaci kwararrun kungiyoyi da dama, kuma yana fatan 'yan wasan keke na Kamaru za su yi koyi da su.
Kungiyoyi 11 da suka zo daga kasashe 10 ne suka halarci gasar ta wannan karon, cikin har da kungiyoyi guda biyu na kasar Kamaru.
Kuma kasashen da suka halarci gasar sun hada da, Kamaru, Ruwanda, Cote d'Ivoire, Morocco, Congo(Kinshasa), Belgium, Faransa, Jamus, Holland da kuma Slovakia. (Maryam)