in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka a arewa maso gabashin Najeriya
2017-03-03 18:23:01 cri

Wasu 'yan kunar bakin wake 3 sun rasa rayukan su da sanyin safiyar Juma'ar nan, yayin da suke kokarin kaddamar da hari a birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA mai kula da yankin arewa maso gabashin kasar Abdulkadir Ibrahim, ya ce daya daga maharan ya tada bam din dake jikin sa ne a wani wuri dake kan titin Damboa, a kusa da wata tankar dakon mai, lamarin da kuma ya haddasa tashin gobara.

Ibrahim ya ce wasu tankokin man biyu sun kone kurmus sakamakon wutar da ta kama, an kuwa kwashe gawawwakin maharan su 3, tare da kashe gobarar da ta tashi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China