Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki, wanda gamayyar kafofin watsa labaru na nahiyar Afirka suka shirya, game da ayyukan tada kayar baya, taron da ya gudana a Abuja fadar mulkin kasar.
Mansur Dan-Ali ya ce yana farin ciki da ganin yadda kungiyoyi masu zaman kan su ke maida hankali, wajen magance tarin matsaloli da wannan yanki ya fuskanta ta fuskar tsaro da yaki da ta'addanci da dai sauran su.
Daga nan sai ya ja hankulan matasa da jam'iyyun gama kasar a kasar, da su sauke nauyin dake wuyan su, na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a dukkanin fadin kasar.
Ya ce yayin da gwamnati ke hankoron ganin ta cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkanin sassan Najeriya, kamata ya yi 'yan kasar su ma, su kauracewa duk wani mataki daka iya haifar da tada husuma, ko kuma yiwa dokokin kasar karan tsaye.(Bello Wang)