in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeria; an sanya dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna bayan barkewar wani rikici
2017-02-22 10:05:09 cri
Jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu lardunanta biyu, domin kare sake tada rikicin da ya barke kwanaki biyu da suka gabata.

Wata sanarwar da majalisar tsaro ta jihar ta fitar jiya, ta ce an dauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyi, da kuma kare sake barkewar rikici a lardunan Kaura da Jema'a, inda rikici ya barke a ranar Lahadi ya kuma ci gaba har zuwa Litinin.

Gwamnatin Jihar ta ce an umarci dukkan hukumomin tsaro su tabbatar da kiyaye dokar.

Duk da kokarin hukumomin Nijeriya na sulhunta bangarorin da ke rikici da juna, tsawon watanni, tsakanin makiyaya da al'ummomin yankin Kaduna ta Kudu yaki ci-ya-ki cinyewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China