Abayomi Olonisakin ya bayyana haka ne jiya a Abuja, yayin bude wani taron yini uku na kwararru daga kasashe mambobin hukumar kula da yankin Tafkin Chadi da Benin.
Ya kuma bukaci rundunar hadin gwiwar ta kara zage damtse wajen murkushe ragowar 'ya'yan kungiyar Boko Haram.
A cewarsa, fatattakar 'yan ta da kayar bayan daga maboyarsu a Nijeriya, ya sa sun bazu, inda suke kai hare-hare yankunan dake karkashin ikon rundunar.
Olonisakin ya ce wannan yunkuri ne na 'yan tada kayar bayan na sake haduwa.
Babban hafsan tsaron ya ce kowace kasa cikin kasashen yankin na amfani da nata dabarun yaki da ta'addanci, sannan kuma suna daukar wasu matakai a tare, yayin da yakin na sojoji ke ci gaba. (Fa'iza Mustapha)