Masanin tattalin arzikin wanda tsohon mataimakin shugaban jami'ar Ghana dake Legon ne, ya bayyana aikin gona a matsayin wani muhimmin fannin wanda za'a iya bunkasa shi cikin karami da matsakaicin zango, kana ya jaddada muhimmancin bunkasa fannin masana'antu wanda galibi yake daukar dogon lokaci.
Ernest ya bayyana a lokacin wani taro da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci a birnin Accra cewa, inganta fannin masana'atun yana da matukar alfanu, bama wajen sarrafa kayan amfanin gona kadai ba, har ma da sauran kayayyakin da ake sayo su daga kasashen ketare a halin yanzu.
Aryeetey yace, game da batun manyan fasahohin da ake bukatar amfani dasu a masana'antun kasar, a cewarsa gwamnatin Ghana zata hada kai da kamfanonin kasashen Sin da Indiya wadanda a shirye suke a koda yaushe su zuba jari a masana'antun kasar.(Ahmad Fagam)