Wasu mahara 7 da sojojin Kamaru 2 sun mutu, a wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram da kaddamarwa a yankin arewa mai nisa na Jamhuriyar Kamaru.
Wata majiya daga rundunar sojin Kamaru wanda ba ta amince a bayyana sunanta ba, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, maharan sun kaddamar da harin ne a wani sansanin sojojin Kamaru dake Soueram, a yankin arewa mai nisa wanda ke iyaka da Najeriya, lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2 na daren Asabar, agogon yankin, sai dai dakarun sojin sun yi nasarar dakile wannan hari.
A binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, 7 daga cikin maharan ne aka tsinci gawawwakinsu a wajen. Majiyar ta kara da cewa Kamarun ta yi hasarar biyu daga cikin sojojinta a lokacin wannan harin.
Sai dai kawo yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin, kana babu wasu bayanai da hukumomin Jamhuriyar Kamaru suka fitar game da wannan hari.(Ahmad)