Dakarun rundunar sojin Nijeriya dake aiki a jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar, sun ceto mutane 211 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Sani Usman ya fitar, ta ce dakarun runduna ta 22 ta Garrison dake aiki karkashin shirin Operation Lafiya Dole, sun ceto mutanen ne yayin wani samame da suka kai kauyukan Cingal Murye da Maja a ranar Asabar.
Nijeriya ta samu nasara a yakin da take da kungiyar Boko Haram, inda a watan Disamban bara, dakarunta dake aiki a yankin arewa maso gabashin kasar suka fatattaki mayakan kungiyar daga dajin Sambisa wanda shi ne sansanin kungiyar mafi girma a kasar.
Jami'an tsaro sun kara matse kaimi wajen aikin sintiri a yankin, inda suka fadada ayyukan na su zuwa iyakokin Niger da Chadi.(Fa'iza Mustapha)