in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boho Haram 15
2017-01-22 12:58:14 cri

A ci gaba da yakin da suke yi da ta'addanci, dakarun Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 15 wadanda ke kokarin hada kai don kaddamar da harin ta'addanci a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarrwa da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Tukur Buratai ya fitar wadda ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Asabar, ya ce guda daga cikin maharin 'dan kasar waje ne, kuma an damke shi ne lokacin da sojojin ke farautar 'yan ta'adda a kauyen Rann, dake yankin Kala Balge a jihar Borno.

Buratai ya ce, an hallaka 'yan ta'addan, kuma wani guda da aka damke yana da hannu wajen haddasa harin nan da sojin samar kasar suka kaddamar kan fararen hula a bisa kuskure a ranar Talatar da ta gabata a wannan gari.

Dakarun Najeriyar sun dakile wani yunkurin harin ta'addanci ne da yammacin ranar Alhamis a kauyen Rann, ya kara da cewa, dakarun Najeriyar sun kwace manyan bindigogi biyu da alburusai wadanda 'yan ta'addan ke amfani da su.

Kimanin 'yan gudun hijira 43,000 ne ke fama da matsalar karancin abinci wadanda ke zaune a sansanin na Rann, inda dakarun Najeriyar suka kai hari bisa kuskure a ranar Talatar da ta gabata.

A kalla mutane 52 ne suka mutu kana mutane 120 suka jikkata sakamakon harin dakarun kasar.

Buratai ya ce, sojojin Najeriya sun koyi darasi sakamakon faruwar wannan lamari, kana ya ce, za su ci gaba da tantance sahihancin bayanai don kaucewa afkuwar hakan a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China