Sannan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasuwanni ya karu da kashi 9.5 idan aka kwatanta da kashi 8.1 a shekarar 2016 a watanni biyun farko na wannan shekara.
Bugu da kari, jarin ajiya da ba'a tabawa na kasar Sin ya karu da kashi 8.9 cikin watanni biyun farko na wannan shekara ta 2017, idan aka kwatanta da kashi 8.1 a shekarar 2016, kamar yadda hukumar kididdiga wato (NBS) ta sanar a yau Talata.