in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana saran tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da daidaita, in ji masana
2017-02-23 21:26:59 cri
Shugaban cibiyar bincike ta majalisar gudanarwar kasar Sin Li Wei ya bayyana cewa, ana saran tattalin arzikin kasar ta Sin zai ci gaba da daidaita a sherkara 2017, duba da yadda gudummawar da sassa daban-daban ke bayarwa kan hakan.

Ana kuma saran bukatun cikin gida za ta karu a shekarar ta 2017,yayin da ake saran samun karuwar zuba jari a bangaren more rayuwa,da bangaren kera kayayyaki wanda shi ma zai fara samun masu sha'awar zuba jari.

Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin taron tuntubar juna game da tsara manufofin kasa na cibiyar da ya gudana a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, ya kuma bayyana cewa,kayayyakin da kasar ta ke fitarwa zuwa ketare shi ma zai bunkasa a wannan shekara ta 2017 da muke ciki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China