Ma Jun ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin wani taron masu ruwa da tsaki game da tattalin arziki da aka gudanar a Singapore. Ya ce manufofin da ake shirin aiwatarwa za su taimaka, wajen daidaita matsayin tattalin arzikin kasar, a gabar da Sin din ke daukar matakai na kara bude kasuwar cinikayyar takardun basukan ta, tare da samar da damammaki na shigar da su cikin gamayyar kasuwannin hannayen jari na kasa da kasa.
Mr. Ma ya kara da cewa, hukumar dake lura da hada hadar musayar kudaden waje, na daukar matakan samar da ka'idoji, wadanda za su bada dama ga masu zuba jari karkashin inuwar bankunan kasashen waje, ta yadda za su shiga kasuwannin musayar kudi na cikin gidan kasar.
Kaza lika ana duba yiwuwar fadada lokutan hada hadar takardun basussuka tsakanin bankuna daban daban, tare da inganta hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin cinikayyar takardun bashin kasar.(Saminu Alhassan)