in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarayyar Afrika ta yi kira da a karfafa hadin kai da kasashen nahiyar dake fama da fari
2017-03-17 09:27:52 cri
Tarayyar Afrika AU ta yi kira da a karfafa hadin kai da kasashen nahiyar dake fama da fari da yunwa.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya a Alhamis, ta ruwaito sabon shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat na cewa, kungiyar ta damu ainun da halin da wasu sassan Afrika ke ciki, sanadiyyar yunwa da fari, wanda shi ne matsalar rashin abinci mafi muni da ake fuskanta a duniya yanzu.

Sanarwar ta ce mutane kusan miliyan 12 ne ke cikin matsanancin bukatar abinci a kasashen Sudan ta Kudu da Somalia da arewa maso gabashin Nijeriya.

Ta kara da cewa, an ayyana matsalar yunwa a wasu sassa na Sudan ta Kudu, al'amarin da ya sanya al'ummar da abun ya shafa a kasar gudun hijira zuwa kasashe makwafta.

A cewar sanarwar, rikice-rikice da rashin tsaro ne suka ta'azzara yanayin da kasashen ke ciki.

Moussa Mahamat ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, su taimakawa al'ummar da abun ya shafa da kudi da kuma wasu abubuwan bukata domin rage musu radadin matsalar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China