in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar tarayyar Afrika ta yi bikin mika mulki ga sabbin shugabanninta
2017-03-15 10:32:29 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU a jiya Talata ta gudanar da bikin mika ragamar shugabanci ga sabbin shugabannin kwamitin kungiyar tare da yiwa jagororin kwamitin kungiyar masu barin gado ban kwana wanda aka gudanar a hedkwatar kungiyar mai mambobi 55 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Da yake jawabi, sabon shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa ya karbi shugabancin kwamitin kungiyar ne a dai dai lokacin da nahiyar Afrika ke fama da kalubaloli masu yawan gaske, sai dai ya nanata aniyarsa na yin aiki tukuri wajen cimma muradun al'ummar nahiyar ta Afrika a tsawon wa'adin aikinsa.

Ya kara da cewa, dimbin kalubalolin da nahiyar ta Afrika ke fama da su sun hada da yawan rikice rikice, yawaitar ayyukan masu tsattsauran ra'ayi, karuwar fatara, rashin ayyukan yi, da kuma gurbacewar muhalli.

Sabon shugaban na kwamitin AU ya ce, manyan batutuwan da zai maida hankali kansu su ne, yin garambawul ga ita kanta kwamitin kungiyar ta AU, da samar da zaman lafiya da tsaro, da batun ci gaban mata da matasa, da bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar, da tabbatar da nahiyar Afrika a matsayin wani muhimmin waje da zai ja hankalin duniya baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China