Wakilin na AU, ya ce yana da tabbaci kan sabon Firayiminstan da aka rantsar a ranar Laraba a birnin Mogadishu wanda nan take ya yi alkawarin inganta yaki da rashin tsaro da cin hanci a kasar.
Francisco Madeira ya ce kwarewar Hassan Khaire a fagen ayyukan jin kai da kasuwanci, muhimman abubuwa ne da za su taimakawa sabuwar gwamnatin.
Ya kuma tabbatar da tawagar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somalia wato AMISOM na aiki tare da sabuwar gwamnatin a daidai lokacin da take kokarin daidaita al'amura ta yadda al'ummar kasar za su amfana.
Francisco Madeira, ya kuma yabawa mambobin majalisar dokokin kasar bisa tabbacin da suke da shi.
Sabon Firaymininsta Hassan Ali Khaire dake da shaidar dan kasa na kasashen Somalia da Norway, na da kwaki 30 da zai nada mambobin majalisar zartarwarsa da za a dorawa alhakin sake fasalta kasar adaidai lokacin da ake tsaka da fama da kalubalen tsaro da fari da cin hanci. ( Fa'iza Mustapha)