in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta jaddada bukatar yaki da mai da yara sojoji yayin rikici
2017-02-24 09:44:18 cri
Kwamitin sulhu na Tarayyar Afrika AU, ya gudanar da wani taron ministoci, inda ya tattauna kan batutuwan da suka shafi mai da yara sojoji yayin yaki.

Yayin taron na jiya da ya gudana karkashin Ministar harkokin wajen Rwanda Louse Mushikiwabo, kwamitin sulhun na AU, ya tafka muhawara kan batutuwa biyu; da suka hada da zirga-zirgar mutane da safarar kayayyaki ba tare da wani tsaiko ba a nahiyar Afrika, da kuma kare yara daga shiga rikice-rikice musammam batun mai da su sojoji yayin da ake yaki.

A jawabinta na bude taron, Mushikiwabo ta ce da yawa daga cikin wadanda ke fada a rikicie-rikicen Afrika yara ne, inda ta ce an kiyasin cewa, kashi arba'in na yara sojoji 'yan Afrika ne, ta na mai cewa ba za a lamunci hakan ba, domin kamata ya yi a ce suna makarantu maimakon kasancewa a bakin daga.

A nasa jawabin, Daraktan kwamitin, Admore Kambudzi, ya ce akwai bukatar kara ba batun kare yara daga shiga rikici muhimmanci, musammam batun yara sojoji, a kokarin cimma muradin ajiye makami da kungiyar AU ke son cimmawa nan da shekarar 2020. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China