in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta amince da komawar Morocco Kungiyar Tarayyar Afrika
2017-02-02 12:47:10 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya ce kasarsa ta amince da sakamakon taron kungiyar AU karo na 28, da ya amince da komawar Morocco cikin kungiyar.

Shugaban wanda ya bayyana haka bayan dawowarsa daga taron da aka yi a birnin Addis Ababa na Habasha, ya ce Afrika ta kudu ta amince ne da nufin karfafa hadin kai a nahiyar.

Cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar, Zuma ya ce kasashe mambobin kungiyar na da ra'ayin cewa, bisa amincewa da kundin tsarin doka, kamata ya yi Morocco ta yi biyayya ga tanade-tanaden doka ta gaggauta warware matsalar dake tsakaninta da yankin yammacin Sahara domin tabbatar da tsaron iyakokinsu.

Bayan doguwar muhawara yayin taron, kasashe mambobin kungiyar hamsin da hudu sun kada kuri'a game da komawar Morocco cikinsu, inda kasashe talatin da tara suka amince.

Sai dai Afrika ta Kudu tare da Zimbabwe da Namibia da Mozambique da Botswana da Algeria sun ki amincewa da batun.

Dukkan kasashen dai sun kasance masu nuna goyon bayan 'yancin kan al'ummar Sahrawi.

Taron dai, ya amince cewa, kungiyar AU za ta ba batun warware matsalar dake tsakanin Morocco da yankin Yammacin Sahara muhimmanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China