in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawaye sun fice daga tsohon birnin Aleppo na kasar Syria
2016-12-07 09:55:02 cri
A jiya Talata 'yan tawaye suka janye daga tsohon birnin dake arewacin Aleppo na kasar Syria, lamarin da ya haifar da fargaba ga shiryyar gabashin birnin.

Gidan talabijin na Pan-Arab Al-Mayadeen ya rawaito cewa, 'yan tawayen sun janye daga tsohon garin na arewaci ne inda suka nausa zuwa wasu sassa na kudu maso gabashi wanda ke makwabtaka da birnin, wadanda har yanzu yankunan na karkashin ikon mayakan 'yan tawayen.

Wata majiya daga dakarun sojin Syria ta tabbatar da cewa, mayakan 'yan tawayen sun janye daga tsohon garin ne bayan sun fuskanci luguden wuta daga dakarun sojin Syria a jiya Talata daga yankin al-Sha'ar mai makwabtaka, yankin dake hannun mayakan al-Qaida mai alaka da kungiyar 'yan tawayen Nusra Front ta gabashin birnin Aleppo.

Kwace yankin na al-Sha'ar ya baiwa dakarun Syriar damar mamaye yankin tsohon birnin na Aleppo da ma sauran sassan birnin baki daya, wanda a baya ya kasance bangarori biyu, guda na hannun 'yan tawayen, guda kuma na hannun gwamnati.

Rida al-Basha, wani dan jarida ne mazauni Aleppo, ya bayyana cewa da ma ana sa ran 'yan tawayen za su janye daga yankin birnin na Aleppo.

Ya ce an gano cewa fararen hula sun fara ficewa daga tsohon birnin, ya kara da cewa an ga wasu motocin bas 6 sun fice daga tsohon birnin na Aleppo cikin dare.

Wani da ya ganewa idonsa faruwar lamarin, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar salula cewa, da yammacin jiya Talata an ji karar harbe harben bindigogi a yankunan arewacin birnin wadanda ke karkashin ikon gwamnati sakamakon ficewar da 'yan tawayen suka yi daga tsohon garin

Bayan munanan hare-haren da dakarun sojin suka kaddamar cikin makonni biyu da suka gabata, sojojin gwamnatin Syria sun kwace iko da kashi 2 bisa 3 na yankunan gabashin Aleppo wadanda ke karkashin ikon 'yan tawayen.

Sama da fararen hula 30,000 ne suka tsere daga yankunan gabashin Aleppo cikin makonni biyu da suka gabata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China