in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare hare ta sama sun kashe mutane 25 a yankin Idleb na Siriya
2016-12-07 10:45:21 cri
A ranar Talata, hare hare ta sama da aka kai a yankunan dake hannun 'yan tawaye, musamman ma a birnin Idleb, dake arewa maso yammacin kasar Siriya, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 25, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Siriya. Wadannan hare hare ta jiragen yaki sun shafi wasu yankunan dake yankin Idleb, a cewar wannan kungiya. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Siriya dake hedkwata a Ingila ta bayyana cewa adadin zai iya karuwa domin akwai yawan mutanen da suka ji rauni mai tsanani. Kungiyar ta kara da cewa akwai yiyuwar jiragen yakin Rasha ne suka kai hare haren ta sama.

Haka kuma, ta nuna cewa a ranar Talata, mutane biyar sun mutu yayin da wasu goma sha biyar suka jikkata a wani luguden wuta da 'yan tawaye suka kai a biranen 'yan Shi'a na Kafraya da Foa dake karkarar Idleb. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China