Wu Haitao, wanda shi ne mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya yi wannan kira ne bayan da kwamitin tsaro na MDD ya kada kuri'ar goyon bayan shirin yarjejeniyar tsakaita bude wutar, da kuma sabon shirin tattaunawar zaman lafiya a tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna, wanda ake sa ran gudanarwa a Astana, babban birnin Kazakhstan.
Wu ya ce kasar Sin tana maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar tsakaita bude wutar, kana ta yaba da ci gaban da aka samu game da sakamakon da aka cimma dangane da bijirewa da kasashen Rasha da Turkiyya suka yi a baya. (Ahamd Fagam)