Da yake jawabi jiya Jumma'a a lokacin taron kasa da kasa na samar da kudaden tunkarar sauyin yanayi wato CFD, Mezouar, ya ce samun dauwwamman ci gaba a nahiyar Afrika ya ta'allaka ne wajen inganta tsare tsaren hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da suka shafi ci gaba mai dorewa da kuma tunkarar batun sauyin yanayi.
Game da wannan batu, ya bukaci kasashen na Afrika su samar da wasu dokoki na musamman da suka shafi yadda za'a samar da kudade don bunkasa ci gaban kanana da matsakaitan masana'antu, musamman wadanda suke da alaka da makamashi marar gurbata muhalli.
Mezouar ya lura cewa, tsarin na CFD, ya zone a adaidai lokacin da aka amince da yarjejeniyar Paris game da sauyin yanayi, a cewarsa wannan wata dama ce da za'a yi nazarin hanyoyin da za su kara samar da kudaden tunkarar sauyin yanayin, da kuma irin rawar da hukumomin kasa da kasa za su taka game da batun sauyin yanayi musamman a nahiyar Afrika.
Mezouar shi ne zai shugabanci COP22, a taron da za'a gudanar na MDD karo 22 game da sauyin yanayi daga ranar 7 zuwa 18 ga wannan wata a birnin Marrakech na kasar morocco. (Ahmad Fagam)