Bayan nasarar da kasar ta cimma wajen aiwatar da dokar a karon farkon a shekarar 2014, sarki Mohammed VI na kasar Morocco, ya bada umurnin a kaddamar da kashi na biyu na dokar kamar yadda aka shirya aiwatarwa a karshen shekarar nan ta 2016.
Kashi na biyu na dokar wanda zai fara aiki nan take bayan kaddamar da ita, na kunshe da sharruda irin na kashin farko, wanda ya shafi mutane dubu 25.
A watan Satumba da ya gabata ne, mahukunta kasar ta Morocco suka ba da sanarwa cewa sun amince da aiwatar da dokar da ta shafi bakin haure da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba tun a shekarar 2013 su kimanin dubu 23.
A cewar ministan cikin gidan Morocco, ma'aikatar ta ba da kididdigar kashi 23 na bakin hauren dake kasar ba bisa ka'ida ba da cewa 'yan gudun hijirar kasar Syria ne, sannan kashi 21 kuma 'yan kasar Senegal ne, yayin da kashi 19 'yan jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ne.
Ma'aikatar ta sanar da cewa, Morocco ta tisa keyar bakin hauren kimanin dubu 5 zuwa kasashensu na asali.
Majiyar ta kara da cewa cikin shekaru 3, hukumomin kasar sun kori bakin hauren 320, da kuma hana wasu dubu 26 da suka yi yunkurin shiga kasar ta kasashen Turai.
A yan shekarun da suka gabata ne, kasar Morocco ta sauya matsayinta, daga kasar dake sallamar bakin haure zuwa kasashen Turai, ya zuwa matsayin kasar dake bada wurin zama ga bakin haure da 'yan gudun hijira daga kasashen hamadar Afrika, da Syria da kuma Iraqi. (Ahmad)