Wata sanarwar da mai tallafawa tsohon shugaban kasar Ghana Joyce Bawah Mogtari ta bayar ta ce, mujallar dake sharhi kan harkokin shugabanci a Afirka(ALM) wadda ta shirya bikin ta ce, akan zabi mutumin da ya lashe kyautar ce bisa la'akari da rawar da ya taka wajen kare martabar nahiyar a idon duniya, tare da nuna shugabanci na gari gami da gudummawar da ya ba da ga ci gaban nahiyar Afirka.
Mujallar ta ce an zabi Mahama ne saboda gudummawar da ya ba da ga ci gaban harkokin demokiradiya a kasar Ghana.
Baya ga wannan lambar yabo, za kuma a baiwa Mahama takardar yabo ta kungiyar 'yan majalisun dokoki bakaken fata daga Georgie a yayin wannan biki.