Sanarwar ta bayyana cewa, a kwanakin baya, an tsananta halin da ake ciki a yankin iyakar kasa a tsakanin Morocco da Mauritania dake kudancin yankin yammacin hamadar Sahara, dakarun Morocco da na jam'iyyar 'yantar da jama'ar yammacin Sahara sun nuna adawa da juna a wadannan watannin da suka gabata.
Guterres ya ce ya damu sosai da batun, inda ya kalubalanci bangarorin biyu da su yi hakuri da juna, tare da daukar matakai da suka dace domin shawo kan matsalar.
Haka zalika, Guterres ya kalubalanci bangarorin biyu da su janye sojoji daga yankin iyakar kasar, tare da samar da hanyoyin hawa teburin sulhu da kuma tabbatar da bin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. (Zainab)