in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya nuna alhinin rasuwar zaunannen wakilin Rasha a MDD
2017-02-22 13:18:22 cri
A jiya Talata ne kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taron musamman don nuna alhini game da rasuwar Vitaly Churkin, zaunannen wakilin kasar Rasha a MDD, wanda ya rasu a shekaran jiya.

Rahotanni na cewa, babban zauren taron kwamitin sulhun ya cika makil da mutane, inda wakilan kasashe mambobin kwamitin, gami da na sauran kasashe, suka tashi tsaye ,inda suka yi shiru na minti 1 don tunawa da marigayi Churkin.

A nasa bangare, wakilin kasar Sin a MDD mista Liu Jieyi, ya ce Churkin kwararren jami'in diplomasiyya ne, wanda yake da kwarewar aiki sosai. Ya kuma ba da gudunmowa ga ci gaban harkokin MDD.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China