in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nanata kudurinta na ci gaba da ba kiwon dabbobin gida a Afrika goyon baya
2017-02-24 10:37:33 cri
Hukumar kula da samar da abinci ta MDD FAO ta jadadda kudurinta na ci gaba da ba bangaren kiwon dabbobin gida a Afrika goyon baya.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da wani shiri na bunkasa harkar kiwon dabbobin gida mai suna 'Afrika Sustainable Livestock 2050' wato ASL2050 a takaice, shugaban hukumar FAO a gabashin Afrika Patrick Kormawa, ya ce kiwon dabbobin gida wani bangare ne na harkokin noma dake samun bunkasa cikin sauri a Afrika, kuma yana daga cikin muhimman shirye-shirye hukumar.

A jiya ne FAO da hadin gwiwar Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID da wasu kasashen Afrika shida ne suka kaddamar da shirin ASL2050 da nufin samar da ingantaccen bangaren kiwon dabbobin gida mai dorewa a Afrika.

Komarwa ya kara da cewa, ayyukan hukumar FAO na gudana ne la'akari da shirye-shiryen da nahiyar Afrika ta fi ba muhimmanci, kamar shirin bunkasa aikin noma na CAADP da yarjejeniyar Molabo.

Da ya ke nanata bangaren kiwon dabbobin gida a matsayin wani jigo ga shirye-shiryen hukumar FAO, Komarwa ya jadadda kudurin hukumar na ci gaba da ba bangaren goyon baya domin samun ci gaba mai dorewa.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China