in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya bukaci mahukuntan Sin da na Amurka da su karfafa hulda a tsakaninsu
2017-02-22 09:12:38 cri
Dan majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, ya yi kira ga mahukuntan kasar Sin da takwarorinsu na Amurka, da su fadada kwazon su wajen bunkasa hadin gwiwa, domin cimma nasarar inganta alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Mr. Yang ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa ta wayar tarho, da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson. Yang ya ce yana fatan kasashen biyu za su amince da sakamakon tattaunawar da suka gudanar ta hanyar kaucewa mummunan sabani, da fito na fito, su kuma rungumi manufar martaba juna, da hadin kai domin cimma moriyar juna, da kuma kara musaya tsakaninsu.

Ya ce akwai bukatar kasashen su maida hankali sosai, tare da yin taka tsantsan game da batutuwa masu sarkakiya.

A nasa bangare Mr. Tillerson cewa ya yi, Sin da Amurka muhimman kasashe ne a duniya, kuma baya ga irin taimako da hadin gwiwar suke yi wajen samar da ci gaba na kashin kai, a hannu guda kuma, hakan na taimakawa zaman lafiyar yankunansu, da ma duniya baki daya.

Mr. Tillerson ya kara da cewa, Amurka na da nufin hada kai da Sin, ta yadda sassan biyu za su kai ga bunkasa amincin dake tsakaninsu, tare kuma da daga matsayin dangantakar su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China