in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe shida ne suka halarci bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow
2017-02-19 12:42:36 cri
Allah ya yi, an rantsar da shugaban kasar Gambia Adama Barrow a jiya Asabar, inda bikin ya samu halartar shugabanni kasashe shida.

Adama Barrow ya maye gurbin Yahya Jammeh da ya shafe shekaru ashirin da biyu ya na mulkin kasar.

Kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ce ta tilastawa Jammeh barin kasar sanadiiyyar kin amincewa da sakamakon zaben watan Decemba da ya yi.

Shugaba Barrow ya ce har abada, Gambia ta sauya, yana mai jaddada cewa, a yanzu al'ummar kasar sun kwana da sanin cewa za su iya dorawa tare da sauke shugabansu daga karagar mulki.

Tarihi ya nuna cewa, Kwanan Adama Barrow uku a duniya a lokacin da Gambia ta samu 'yancin kai. A yanzu Shekaru hamsin da biyu bayan nan, an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar na uku.

A jawabinsa karo na biyu, ya yi alkawarin magance kalubalen zaman takewa da tattalin arziki da ake fuskanta a kasar da suka shafi kiwon lafiya, ilimi, har ma da dagantaka da kasashen ketare da kuma sulhunta rikicin cikin gida.

Shugabannin kasashe shida da suka halarci bikin rantsuwar sun hada da Ellen Sirleaf Johnson ta Liberia da Nana Akufo-Addo na Ghana da Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire da Roch Marc Christian Kabore na Burkina Faso da Macky Sall na Senegal da kuma Abdel Aziz na Mauritania. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China