A dai ce wadannan shirye-shirye da 'yan majalisar suka gabatar, sun shafi kara gudanar da kwaskwarima ga tsarin sa ido na kasa, da kyautata dokokin dake da nasaba da kafa sabon tsarin bunkasuwa, da bunkasa siyasar demokuradiyya bisa tsarin gurguzu, da bunkasa sha'anin al'adu, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma inganta muhalli da dai sauransu.
Baya ga haka, 'yan majalisar sun kuma gabatar da shawarwari dangane da muhimman batutuwan da suka shafi yin gyare-gyare, da bunkasuwa, da kuma wasu batutuwan da ke jawo hankulan jama'ar kasar, kuma shawarwarin da aka samu sun kai 8360, a kuma yanzu haka ana kokarin zabar hukumomin da abin ya shafa, don su tabbatar da shawarwarin. (Bilkisu)