A yayin tattaunawar, shugabanni sun ba 'yan majalisun kwarin gwiwar sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata, tare da kara himmantuwa wajen ba da shawarwari ga kasa, da gudanar da ayyuka a fannonin inganta yin kwaskwarima, neman ci gaba, inganta walwalar jama'a, da kuma hada kan jama'ar kabilu daban-daban don kokarin cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin.
Tun bayan babban taron wakilai karo na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kwamitin tsakiyar jam'iyyar ya mayar da hankali sosai kan ayyukan kananan kabilu, da kuma bunkasar yankunan kabilun.
Shugaba Xi Jinpin sau da yawa ya kai rangadi a yankunan kabilu, don fahimtar yadda rayuwar jama'a kananan kabilu ya ke, tare da kuma tsara shirin inganta rayuwarsu. (Bilkisu)