in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta lashi takobin yaki da yanke hukunci bisa kuskure
2017-03-12 14:05:43 cri
Rahoton aikin kotun kolin jama'ar kasar Sin ya ce hukumomin shari'a a kasar, sun lashi takobin daukar darasi daga hukunce-hukunce da aka yanke bisa kuskure, tare da tabbatar da ba a sake aiwatar da su ba, a kokarin da ake na daukaka tsarin shari'a.

A cewar rahoton aikin da babban jojin kasar Zhou Qiang ya gabatar ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, tafka kuskure wajen yanke hukunci na zubar da kimar bangaren shari'a, sannan kuma akwai darrusa da za a iya dauka.

Rahoton ya ce jimilar mutane 1,076 ne ba a same su da laifi ba cikin shari' un da aka yi a bara, inda ya ce kotuna a dukkan matakai sun matse kaimi wajen tantance shari'u, inda bayan sake gudanar da wasu shari'u aka gyara shari'un 1,376 da aka riga aka yanke.

A rahoton da ya gabatar, mai gabatar da kararraki a kotunan kasar Sin Cao Jianming, ya ce hukumomin gabatar da kararraki sun yi nazarin shari'u masu matsala, sun kuma gyara kurakuren dake akwai tare da himmantuwa wajen sake nazari da tantance hukunce-hukunce domin tabbatar da adalci a kowacce shari'a.

Ya ce hukumomin shigar da kararraki a fadin kasar za su koyi darasi daga matsalolin da aka samu wajen shigar da kara da nufin inganta ayyukansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China