Da yake karin haske kan wannan batu a lokacin da yake gabatar da rahoton aikin kotun kolin al'umma yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar Sin da ke gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, babban mai gabatar da kara na kasar Cao Jianmin ya bayyana cewa, an tuso keyar wannan adadi ne daga kasashe da yankuna 37.
Wadannan a cewarsa, sun hada da mutane 27 wadanda ke cikin jerin sunayen da 'yan sandan kasa da kasa ke nema ruwa a jallo. Akwai kuma wasu mutane 3 cikin mutane biyar din da kasar Sin take nema ruwa a jallo wato Yang Xiuzhu da Wang Gouqiang da Huang Yurong da suka guda zuwa kasar Amurka amma daga bisani suka mika kansu ga hukumomin kasar Sin, yayin da shi kuma Li Huabo aka tuso keyarsa zuwa kasar Sin daga kasar Singapore.
Tun a shekarar 2003 ne dai Yang Xiuzhu tsohuwar darektan hukumar kula da gine-gine na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin ta bar kasar Sin ta gudu bayan da sifetocin yaki da cin hanci suka fara bincikarta bisa zarginta da hannu da almabozzaranci da kudaden jama'a.
A ranar 16 ga watan Nuwanban shekarar 2016 ne ta mika kanta ga mahukunta. (Ibrahim)